Loading ...
Sorry, an error occurred while loading the content.
 

ENGR. MOHAMMED BASHIR KARAYE HAUSA LITERITURE CONTEST

Expand Messages
 • elhajeej maje
  Ko shakka babu duk wani marubucin da yake rubutu da harshen Hausa, zai kasance mai matuk’ar farin ciki mara misaltuwa a yayin da ya halarci taron karrama
  Message 1 of 1 , Oct 25, 2007
   Ko shakka babu duk wani marubucin da yake rubutu da harshen Hausa, zai kasance mai matuk’ar farin ciki mara misaltuwa a yayin da ya halarci taron karrama marubutan Hausa da akayi a INTERNATIONAL CONFERENCE CENRE dake birnin tarayyar Abuja wanda Hajiya Bilkisu A. Bashir  ta d’auki nauyi domin tunawa da maigidanta Engr. Mohammed Bashir Karaye daya rasu, tare da had’in gwiwar k’ungiyar marubuta ta k’asa reshen jihar Abuja, da yammacin ranar alhamis 25 ga oktobar 2007(ENGR. MOHAMMED BASHIR KARAYE HAUSA LITERITURE CONTEST)
               A tarihin rubutun Hausa wannan itace gasa mafi k’ayatarwa da na tab’a gani, wacce aka gabatr cikin kyakkyawan tsari da kuma ingantattun kayan aiki na zamani. Abu na farko mafi k’ayatarwa shine irin manyan mutanen da suka halarci taron ciki harda alk’alin alk’alai na tarayya, Hon. Justice Idris Legbo Kutigi, CON tare da tsohon alk’alin alk’alan kuma shugaban kwamitin tsarkake  harkokin zab’e wato Hon. Justice M.L. Uwais, GCON Sannan kuma yadda kafafen yad’a labarai suka d’inke wajen, jaridu na turanci da Hausa, gidajen radiyo na gida dana k’etare. Banda masu hoto da suka walwala mana hasken na’urorinsu kamar  ‘yan sama jannatin da suka yi nasarar saukowa lafiya daga duniyar Mercury!
               Abin sha’awa shine da zarar an kira sunan marubuci sai hoton bangon littafinsa ya bayyana a majigin da ke jibge k’auye guda. Kana kuma ga abin Magana rad’au kamar me! Wani babban abin birgewa shine yadda duk wad’annan manyan mutanen da suka taru domin karrama marubuta littattafan Hausa akwai wad’anda gaba da baya Hausawa ne, wasu ma suna da gidajen yad’a labarai da yake janyo musu mak’udan kud’d’e da harshen Hausa’ amma su basu tab’a tunanin yin irin wannan hob’b’asa ba.
               Bugu da k’ari abincin ma da aka ci a wajen wani abu ne na daban, baya ga irin mutanen da suka rik’a karb’ar lambar wayar mu, wad’anda mutum bazai tab’a tunanin zai had’u das u a zahiri ba. A tak’aice wannan gasa koda babu wani abu da za’a bawa mutum abin alfahari ne, domin a ranar ne na fahimci hak’ik’anin darajar da marubucin Hausa yake da ita. Kuma a wannan rana ne na ji wani k’warin gwiwa tare da zage damtse na ci gaba da inganta ayyukana, kana kuma na hana idona barci don ci gaba da yad’a harshen Hausa a duniya.
               Littafin ‘Yartsana na marubuci Ibrahim Sheme ne ya zo na farko, yayin da Matar Uba Jaraba na Hajiya Balaraba Ramat ya zo na Biyu, kana kuma Kankana na marubuci Maje El-Hajeej Hotoro yazo na uku.
               Godiya ga wannan baiwar Allah da kuma wad’anda suka bayar da gudunmawa wajen ganin komai ya kamala, daga k’arshe ina mik’a ta’aziyyata ga d’aya daga cikin alk’alan wannan gasa Farfesa Abdallah Uba Adamu, wanda ina cikin d’akin taron ne bayan na shagaltu da hange-hangen inda yake na tsinkayi labarin rasuwar mahaifiyarsa daga bakin Sheme. Kuma abinda ya bani mamaki shine yadda kusan biyu na rana muka yi waya das hi bai fad’a min ba, face sai murna da yayi min na fitowar littafina a cikin jerin uku da suka tsallake sharud’d’an cin gasar da aka gindaya.

   __________________________________________________
   Do You Yahoo!?
   Tired of spam? Yahoo! Mail has the best spam protection around
   http://mail.yahoo.com

  Your message has been successfully submitted and would be delivered to recipients shortly.